Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta kama Darius Ishaku tsohon gwamnan jihar Taraba kan zargin al-mundahanar kuɗaɗen da yawansu yakai biliyan 9.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Ishaku na can tsare a ofishin hukumar dake Abuja.
Duk da cewa mai magana da yawun hukumar ta EFCC ya tabbatar da labarin amma bai bada ƙarin gaske ba kan batun.
A ranar Alhamis ne hukumar ta EFCC ta shigar da ƙara a gaban babban kotun tarayya dake Abuja inda takewa tsohon gwamnan tuhume-tuhume 15.
Ishaku ya mulki jihar Taraba daga shekarar 2015 ya zuwa 2023.
A cikin watan Yulin shekarar 2023 hukumar EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan kan binciken da take yi akan yadda ya mulki a jihar a tsawon shekaru 8 da ya shafe akan kujerar mulkin jihar.