Hukumar EFCC ta samu nasarar damke Akanta Janar na Najeriya, Alhaji Ahmad Idris.
EFCC na zargin sa da karkatar da kudaden da yawansu ya kai naira biliyan 80 ta hanyar bada kwangilolin bogi ga iyalai da wasu makusantansa.
A sanarwar da hukumar ta EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook ta zargi Idris da kin amsa gayyatar da tayi masa bayan da bayanan sirrin da ta samu sun nuna ya mallaki wasu kadarori a Kano da kuma Abuja.