Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta cafke wasu mutane 31, ciki har da Sinawa hudu, bisa zargin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Jos, babban birnin Jihar Filato.
Mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja.
A cewar sanarwar, an kama mutanen ne a ranar Asabar a harabar kamfanin Jiasheng Nigeria Limited da ke Dura Rayfield, kan titin Mangu a Jos.
Oyewale ya ce kama su ya biyo bayan samun sahihan bayanai da suka danganta kamfanin da ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar.
Ya bayyana cewa cikin mutanen da aka kama, akwai Sinawa hudu da kuma ‘yan Najeriya 27 da ke da hannu a harkar, ciki har da masu kawo ma’adanai da ba a tace ba, wadanda ake zargin an hako su ne ba bisa ka’ida ba.
Haka nan, hukumar ta ce ta samu wasu kayayyakin shaida a wurin, ciki har da wata motar daukar kaya cike da buhuna takwas na Monazite da aka tace, wanda kowanne buhu ke da nauyin kilogiram 1000. Ana kiyasta darajar kowanne buhu a kan naira miliyan hudu.
EFCC ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargi a kotu da zarar an kammala bincike.
EFCC Ta Cafke Ƴan China 4 Da Wasu 27 Kan Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba a Jihar Filato
