Hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa da tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta fara binciken tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso kan zargin yin almundahana da kuɗaɗen fansho.
Wata majiya dake hukumar ta EFCC ta faɗawa jaridar The Cable cewa an karkatar da kuɗaɗen ne daga asusun gwamnatin jihar Kano lokacin da Kwankwaso yake mulkin jihar.
Majiyar ta ce gidajen da ya kamata ace an bawa ƴan fanshon a wancan lokacin su ne aka bawa wasu mutane daban.
“Akwai lokacin da ƴan fansho suka biya kuɗi domin mallakar gidaje kuɗin ya kai biliyan 2.5 amma aka karkatar da kuɗaɗe lokacin gwamnatin Kwankwaso kuma aka hana su gidajen,” a cewar majiyar.
“An bawa wasu mutanen na daban gidajen amma mun ƙwato gidajen mun bawa ƴan fanshon,”
Majiyar ta ƙara da cewa duk da cewa sun ƙwato gidajen suna cigaba da bincike saboda an riga an aikata laifi tun da farko.