ECOWAS Ta Yi Allah-wadai Da Yunkurin Juyin Mulki a Benin

Hukumar ECOWAS ta bayyana damuwa kan bayanan da suka fito game da yunkurin kifar da gwamnati da aka yi a Jamhuriyar Benin. Ta ce lamarin abu ne mai tsanani kuma ya sabawa zabin jama’a.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Lahadi, ECOWAS ta yi Allah-wadai da wannan mataki da ta kira ba bisa ka’ida ba. Ta kuma bukaci a mutunta kundin tsarin mulkin kasar.

Hukumar ta yaba wa gwamnatin Benin da rundunar sojin Republican Army bisa tabbatar da cewa an dawo da daidaito da kwanciyar hankali.

ECOWAS ta gargadi wadanda suka hada kai wajen kitsa wannan yunkuri. Ta ce za su dauki nauyin duk wani abin da zai jawo asarar rai ko dukiya.

Ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da tallafa wa gwamnatin Benin da al’ummar kasar ta kowane fanni. Hakan ya hada da yiwuwar tura rundunar hadin gwiwar yankin domin kare kundin tsarin mulki da kuma iyakokin kasar.

More from this stream

Recomended