Duniya na alhinin mutuwar Kofi Annan

[ad_1]

Mr Annan

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

An dauki hoton Mr Annan ne wata guda kafin mutuwar sa.

Shugabannin kasashen duniya da ‘yan siyasa da kuma jami’ai daga bangarori daban-daban na duniya na alhinin mutuwar tsohon shugaban majalisar dinkin duniya, Kofi Annan.

Mr Annan ya rasu ne ranar Asabar bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya, a cewar Gidauniyar the Kofi Annan Foundation.

Babban ma’aikacin diflomasiyyar, wanda dan asalin kasar Ghana ne, ya mutu ne a birnin Geneva, inda ya kwashe shekara da shekaru yana zama.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwan Mr Annan bisa wannan babban rashi da duniya ta yi.

A cewar sa, tsohon shugaban majalisar dinkin duniyar ya “ya daukaka sunan kasarmu sabida mukamin da ya rike da kuma halayensa a duniya. Shi mutum ne da da ya yi amanna cewa duk dan kasar Ghana zai iya zama abin da yake son zama idan ya zage damtse.”

A nasa bangare, shugaban majalisar dinkin duniya, António Guterres, ya ce Kofi Annan “mutum ne da ya jagoranci samar da abubuwa masu kyawu. Na bi sahun duniya wajen alhinin rashin sa. Nasarorin da ya samu wajen samar da zaman lafiya za su zamar mana abin koyi a wannan duniya mai cike da rudani.”

A sakon da shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki, ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce marigayi Kofi Annan “mutum ne jajirtace wanda ya kasance mai kare hakkin mutanen da ba su da galihu, kuma ma’aikacin diflomasiyya ne wanda ya yi aiki tukuru domin samar da zaman lafiya a wannan duniya mai cike da matsaloli.”

Shi ma gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya ce “Nahiyar Afirka ta yi rashin daya daga cikin manyan ‘ya’yanta, kuma duniya ta yi rashin mutumin kirki.”

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar marigayi Mr Kofi Annan ya bar Kofi Annan “ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban dan adama kuma ba za a taba mantawa da shi ba.”



[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...