DSS Ta Kama Mutane Biyu Bisa Zargin Yaudarar Jama’a Da Sunan Daukar Ma’aikata a Kaduna

Hukumar tsaron farin kaya, wato DSS, ta cafke wasu mutane biyu a Kaduna bisa zargin kafa kungiya ta bogi da ke yaudarar jama’a da sunan daukar ma’aikata cikin hukumar.

Wadanda aka kama sun hada da Aliyu Ibrahim da wani abokinsa, bayan samun bayanan sirri da suka tona musu asiri.

Binciken farko ya nuna cewa tsakanin mutane 250 zuwa 350 na iya kasancewa sun fada tarkonsu, inda aka musu alkawarin samun aiki a DSS.

Wani majiyar tsaro ya tabbatar da cewa ana tsare da wadanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bin sawun sauran mambobin kungiyar.

DSS ta ja hankalin ‘yan Najeriya da su yi hattara da irin wadannan shirin daukar aiki na bogi, tana mai jaddada cewa duk wani daukar ma’aikata na hukumar ana sanar da shi ne ta hanyoyin hukuma kawai.

Hukumar ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da bayar da rahoton duk wata motsi mai kama da na zamba ga hukumomin tsaro.

More from this stream

Recomended