Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS sun kama wani mutum dake ɗauke da kudade a cikin motarsa da ake kyautata zaton zai yi amfani da su ne wajen sayen kuri’a a zaɓen gwamnan jihar Ondo da ake yi.
An kama mutumin ne a lokacin zaɓen a mazaɓa ta 4 akwatu 007 dake wajen makarantar firamaren St Stephen dake Akure babban birnin jihar.
Wani fefan bidiyo da aka ɗauka ya nuna yadda mutane da jami’an tsaro suka matsa mutumin kan lallai sai ya buɗe but ɗin motarsa.
Bayan da ya buɗe ne aka ga jaka biyu Ghana mastigo a ajiye a ciki but ɗin, buɗewarsa ke da wuya sai jami’an tsaron suka wurga shi a motarsu suka yi gaba da shi.
A ranar Asabar ne 16 ga watan Nuwamba ake gudanar da zaɓen kujerar gwamnan jihar.