Hassanal Bolkiah, Sultan na kasar Brunei, ya mayar wa Jami’ar Oxford digirin karramawa da ta ba shi saboda sukar da ya sha bayan ya kaddamar da hukuncin kisa kan ‘yan luwadi da ma’aurata mazinata a fadin Brunei.
Kusan mutum 120,000 ne suka rattaba hannu kan wani korafi na neman jami’ar da ta soke digirin da ta karrama shi da ita a shekarar 1993.
Jami’ar ta Oxford ta tabbatar da cewa dai Sultan din shi da kansa ya yi niyyar dawo masu da digirin.
A kwanakin baya ne dai Hassanal Bolkiah ya kaddamar da dokokin kisa kan duk wanda aka kama da laifin luwadi ko mai aure da aka kama yana zina.
Sai dai bayan kaddamar da dokar, Sultan din ya sha suka daga Majalisar Dinkin Duniya da ma taurari, cikinsu har da George Clooney.