Shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Yakubu Dogara ya ziyarci sakatariyar jam’iyar APC dake Abuja bisa rakiyar wasu manyan yan siyasar jihar Bauchi a yau ranar Alhamis.
Yakubu Dogara ya yi amfani da ziyarar wajen sanar da ficewarsa daga jam’iyar APC mai mulki.
“Na yanke shawarar na dawo,” Dogara ya fadawa dandazon jama’ar da suka taru wadanda suke cikin murna.
Haka kuma ya mikawa jam’iyar fom dinsa na tsayawa takara a karkashin jam’iyyar da mutanen mazabarsa suka saya masa.
Tun lokacin da shugaban majalisa dattawa Abubakar Bukola Saraki ya fice daga jam’iyar ta APC masu lura da al’amuran yau da kullum ke ganin lallai Dogara shima zai fice daga jam’iyar ka wai dai yana jiran lokacin ya yi.
Sauya shekar tasa baya rasa nasaba da takun sakar dake tsakaninsa da gwamnan jiharsa ta Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar.