Direban tanka ya ƙone ƙurmus a Ibadan

Wata motar tanka dake ɗauke da manfetur ta yi bindiga ta kama da wuta a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo abun da ya kai ga konewar direban motar ƙurmus.

Yemi Akinyinka shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Oyo ya ce lamarin ya faru a ranar Laraba akan babban titin Iwo.

Ya ce tankar motar ta ƙwace inda ta ci karo da wasu motoci biyu kafin ta tuntsura cikin wani rami inda ta kama da wuta.

Akinyinka ya ce direban motar ya mutu  amma an samu nasarar ceto yaron motar da ransa.

“Lamarin ya faru a wajejen Fisabi House dake Agbowo akan babbar hanyar zuwa Iwo. Hukumar ta samu kiran kai ɗaukin gaggawa da misalin ƙarfe 02:45 na dare kan dake cewa akwai wuta tana ci,” ya ce.

Ya ce jami’an hukumar sun yi gaggawar zuwa wurin inda suka taimaka wajen hana wutar bazuwa.

More from this stream

Recomended