Daraktan kula da gidan tarihin Auschwitz, tsohon sansanin ƴan Nazi a Poland ya yi tayin zaman gidan yari na hukuncin ɗaurin shekara 10 da aka yanke wa wani yaro ɗan Najeriya mai shekara 13 da ya zagi Allah a Kano.
Dakta Piotr Cywinski, ya ce shi da wasu ƴan sa-kai 119 daga sassan duniya za su yi wa yaron zaman gidan yari na wata ɗaya ko wannensu.
A watan Agusta ne kotun shari’ar musulunci ta yanke wa yaron hukunci kan wasu kalamansa da ba su dace game da Allah yayin wata muhawara da abokinsa a jihar Kano
Lauyan yaron ya ɗaukaka ƙara, yana cewa hukuncin ya saɓa wa ƴancin yara da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya. Ya shaida wa BBC cewa har yanzu ba a sa ranar sauraren ƙarar da ya ɗaukaka ba a kotun.
Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohi 12 a Najeriya da ke bin tsarin gwama shari’ar musulunci da dokokin ƙasa.
Asusun kula da yara ƙanana na Majalisar Ɗinkin Duniya Unicef, ya yi kira ga hukumomin Najeriya su gaggauta sake duba hukuncin.
Me daraktan gidan tarihin Auschwitz Memorial ya ce?
A cikin wasiƙar da ya aika wa Shugaba Buhari, Dakta Cywinski, ya rubuta cewa a shirye yake ya yi wa yaron zaman gidan yarin.
“Ba tare da la’akari da abin da ya faɗa ba, ba za a iya ɗaukar shi mai cikakken hankali ba, saboda shekarunsa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan har ba za a yafe wa yaron ba, shi da wasu ƴan sa-kai 119 za su yi masa zaman gidan yarin.
Ya kuma ce za su ɗauki nauyin karatun yaron.
Gidan tarihin na Auschwitz bai cika tsoma baki ba a irin wannan batu.
Zuwa yanzu gwamnatin Najeriya ba ta ce komi ba game da batun
Gidan tarihin na Auschwitz-Birkenau, tsohon sansaani ne na ƴan Nazi a Poland inda aka kashe mutum miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya, kuma kusan mutum miliyan ɗaya da aka kashe Yahudawa ne.