Darajar naira tayi kasa bayan sanar da sauya fasalin kudi

Darajar takardar kudin naira tayi kasa a kasuwar musayar kudaden waje.

Tuni dai masana da dama suka yi hasashen haka tun bayan da babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da sanarwar shirinsa na sauya fasalin takardar kudin naira.

Masanan sunyi hasashen cewa mutanen da suka boye kudade a gidajensu za su fito da su domin canza su ya zuwa dalar amurka mai makon su kai asusun su na banki.

A kasuwar musayar kudade ta bayan fage a Abuja an rika sayar da dala kan 775 inda ake sayarwa kan 781.

Hakan na nufin an samu karin kaso 2.64 cikin dari idan aka kwatanta da yadda ake sayarwa a baya.

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...