Darajar Naira tayi kasa a kasuwar musayar kuɗaɗe

Farashin Naira yayi kasa zuwa 620 kan kowace dalar Amurka 1 a kasuwar musayar kudade ta bayan fage a yayin da ake cigaba da fuskantar karancin kudaden kasashen waje.

Hakan na nufin darajar naira tayi kasa da ₦5 ko kuma kaso 0.8 cikin dari kan yadda aka yi musayar ta a makon da ya wuce.

Masu musayar kuɗi a Lagos sun bayyana cewa an samu karin bukatar kudaden ƙasashen waje a kasuwar bayan fage daga masu shigo da kaya daga waje.

Masu musayar kudin sun ce sun saya akan ₦614 su sayar 620.

Sai dai farashin gwamnati yayi kasa da kaso 0.36cikin dari inda ake sayar da dala guda kan ₦424.58.

More from this stream

Recomended