Darajar naira ta yi sama a kasuwar musayar kuɗaɗe

Darajar naira ta yi sama a ranar Juma’a inda aka riƙa musayar ta ₦1770 kan dalar Amurka ɗaya a kasuwar bayan fage.

Hakan na nufin darajar ta naira ta karu da naira ₦90 ko kuma da  kaso 4.84 cikin ɗari idan aka kwatanta da yadda aka riƙa musayar ta ranar Alhamis 21 akan naira ₦1860 duk dala ɗaya.

Masu kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe wato Bureau De Change sun ce suna sayan dala ɗaya akan 1730 su kuma sayar akan 1770 inda suke samun ribar  ₦40.

Sai dai kuma a kasuwar bankuna darajar takardar kuɗin ta naira tayi ƙasa da kaso 5.99 cikin ɗari inda aka riƙa canza dalar Amurka ɗaya kan ₦1665.50 a ranar Juma’a maimakon ₦1571.31 da aka sayar da ita a ranar Alhamis.

More from this stream

Recomended