Darajar naira ta ƙara faɗi

Duk da yunƙurin da babban bankin Najeriya ya yi na karfafa kasuwar canji, naira ta rufe kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Investor & Exporter a ranar Alhamis a kan N996.75/$.

Wannan raguwar kashi 13.95 ne daga N874.71/$ da ta rufe kasuwar a ranar Laraba.

Ya zuwa yanzu dai, Naira ta yi asarar kashi 27.75 na darajarta tun bayan farkon mako a kan N780.23/$ bisa ga cikakken bayani kan musayar kudaden da ake samu na FMDQ OTC.

Naira ta yi asarar kusan kashi 40 cikin 100 na darajarta a shekarar 2023, inda ta samu shedar daya daga cikin mafi munin kuɗaɗe na Afirka a bankin duniya.

More from this stream

Recomended