
Takardar kuɗin naira a ranar Juma’a ta kara daraja a kasuwar bayan fage.
Darajar kuɗin na naira ta karu da naira 145 kusan kaso 12.2 cikin 100 inda ake canza dala ɗaya akan naira 1045 kasa da yadda aka canza ta da 185 a ranar Talata.
Wasu masu sana’ar canjin kuɗi a garin Lagos sun ce suna sayan dalar Amurka akan naira 1000 su sayar akan 1040 ribar naira 40 kenan akan kowace dala.
Karuwar darajar naira dai baya rasa nasaba da yadda babban bankin kasa na CBN ya samar da dalar Amurka ga bankuna.