
Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirika kuma shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote ya ce kamfanin ya sanya hannu kan yarjejeniyar zuba jarin dalar Amurka biliyan $1 a fannin siminti da kuma makamashi a kasar Zimbabwe.
Dangote ya yi magana da yan jaridu bayan da ya gana da shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ranar Laraba a birnin Harare.
Hamshakin mai kudin ya ce ya sanya hannu ne akan yarjejeniyar a madadin kamfanin Dangote domin gina kamfanin siminti, tashar wutar lantarki da kuma shinfida bututun mai.
Dangote ya ce yawan kuɗin jarin da zai zuba ya kai Dalar Amurka biliyan ɗaya saboda batutun man da za a shimfida ya kuma kara da cewa akwai kuma ƙarin wasu ayyukan zuba jari da za su yi a kasar.

