Dan majalisar wakilan tarayya na jam’iyar Labour ya koma PDP

Hon. Dennis Agbo, mamba a majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar mazabar Igbo-Eze North/Udenu ta jihar Enugu ya fice daga jam’iyar Labour Party inda ya koma jam’iyar PDP.

Agbo wanda ke zango na biyu a majalisar ya alakanta komawarsa jam’iyar PDP da irin kokarin da gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah yake yi da kuma rikicin cikin gida a jam’iyar LP sai kuma matsin lamba daga al’ummarsa.

A yan kwanakin nan dai ana cigaba da samun yan majalisun tarayya dake cigaba da sauya sheka galibi ya zuwa jam’iyar APC mai mulki amma kuma sai aka samu akasin haka a wurin Mbah.

More from this stream

Recomended