
Yusuf Galambi, mamba a majalisar wakilai tarayya ya sauya sheƙa daga jam’iyar NNPP ya zuwa jam’iyar APC mai mulki.
Tajuddeen Abbas, Kakakin majalisar wakilai ta tarayya shi ne ya sanar da sauya sheƙar Galambi a wata wasika da ya karantawa zauren majalisar a ranar Alhamis.
Galambi na wakiltar ƙaramar hukumar Gwaram a majalisar.
Ya bayyana cewa matakin da ya dauka na sauya sheƙar ya samo asali ne daga umarni da mutanen mazaɓarsa suka bayar.
Galambi shi ne na baya bayan a cikin jerin ƴan majalisar wakilai ta tarayya da suka sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC mai mulki.