Dan majalisar wakilai daga jihar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP ya zuwa APC

Ɗan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Kebbi, Salisu Garba Koko ya sauya sheƙa daga jam’iyar PDP ya zuwa jam’iyar APC.

Koko wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Besse/Maiyama  ya bayyana sauya sheƙar ne a wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas aka kuma karanta ta a zauren majalisar.

A cikin wasikar dan majalisar ya bayyana cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyar PDP shi ne dalilin da yasa shi sauya shekar.

Sauya shekar ta Koko na zuwa ne bai fi sa’o’i 24 ba bayan da ɗan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Kaduna, Amos Gwamna Magaji ya sanar da fitarsa daga jam’iyar ta PDP.

Shugaban marasa  rinjaye a majalisar wakilan, Kingsley Chinda ya nuna ƙin amincewar sa da sauya sheƙar inda ya ce babu wani rikici dake addabar jam’iyar tasu ta PDP..

Ya yi kira ga kakakin majalisar da ayyana kujerar Koko a matsayin babu kowa akai saboda sauya sheƙar.

More from this stream

Recomended