
Mark Esset dan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar, Akwa Ibom ya sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa APC mai mulki.
Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu shi ne ya sanar da sauya shekar Esset a zauren majalisar a yayin zaman da ya jagoranta a ranar Talata.
Esset na wakiltar al’ummomin kananan hukumomin Uyo/Uruan, Nsit Atai/Ibesikpo Asutan a majalisar wakilan ya alakanta sauya shekar tasa da rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyar PDP a matakin kasa.
Ya ce ya sauya shekar ne bayan da ya tattauna da mutanen mazabarsa.
Bayan ficewarsa daga jam’iyar ta PDP a yanzu jam’iyar PDP bata da dan majalisar tarayya ko daya daga jihar Akwa Ibom.
A farkon wannan watan ne yan majalisar wakilai 6 daga jihar ta Akwa Ibom suka koma jam’iyar APC daga PDP.
Yan majalisar sun sauya shekar ne bayan da gwamnan jihar, Umo Eno ya fice daga jam’iyar PDP inda ya koma APC.