Dan Majalisar Dokoki a Jihar Filato Ya Shaƙi Iskar Ƴanci

Dan majalisar dokokin jihar Filato mai wakiltar mazabar Pankshin ta Kudu, Hon. Laven Denty Jacob, ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da shi bayan da aka sace shi a gidansa da ke Jos.

Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai, Hon. Kwarpo Sylvanus, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa dan majalisar ya koma tare da iyalansa lafiya.

“Ana iya cewa an sake shi cikin nasara, amma har yanzu ba mu tabbatar ko an biya kudin fansa ba. Abin da muka sani shi ne an sako shi da daddare jiya,” in ji Sylvanus.

Ya ƙara da cewa dan majalisar ya dawo gida cikin koshin lafiya.

Sylvanus ya roƙi al’umma su kasance cikin shiri da faɗakarwa tare da bayar da rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba a unguwanninsu.

Haka kuma ya yaba da irin jajircewar jami’an tsaro da ‘yan ƙasa wajen mayar da martani cikin gaggawa, inda ya ba da shawarar a kafa ƙungiyoyin sa-kai a al’ummomi don ƙara tsaro.

“Mu a matsayinmu na ‘yan majalisa, za mu ci gaba da fafutukar samar da dokokin da za su ƙarfafa tsarin tsaro a jihar,” in ji shi.

An dai sace Hon. Jacob ne a daren Litinin a gidansa da ke Anguwan Kagji, unguwar Dong, a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa. Wannan lamari ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu mutane biyu — wani ɗan bautar ƙasa da ɗalibin jami’ar Jos — aka yi garkuwa da su a yankin cikin kwanaki goma da suka wuce, lamarin da ya ƙara tayar da hankula kan matsalar tsaro a Filato.

More from this stream

Recomended