Dalilin da yasa na gana da Obasanjo -Saraki

[ad_1]
Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana dalilin da yasa ya kai wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ziyara a gidansa dake Abeokuta a jihar Ogun.

Da yake magana da manema labarai bayan ganawar sirrin da suka yi, ya ce ya ziyarci, Obasanjo ne saboda bai samu damar halartar wurin bikin bude dakin karatu da aka yi mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library.

Ya ce: “kunsan cewa ban samu damar halartar wurin bikin bude dakin karatun ba shi yasa yanzu na yanke shawarar zuwa na gani da ido na a zahirin gaskiya wurin ya kayatar.Muna alfahari da abinda ya yi anan.”

Lokacin da yan jaridu suka tambaye shi kan rikicin dake faruwa a majalisa da kuma yaushe majalisar za ta sake zama Saraki ya yi shiru inda ya shige cikin motarsa da sauri.
[ad_2]

More News

Wani mahajjacin Jihar Filato ya riga mu gidan gaskiya a Makka

Allah ya yi wa wani mahajjacin jihar Filato Ismaila Musa rasuwa a birnin Makka na kasar Saudiyya.Daiyabu Dauda, babban sakataren hukumar jin dadin alhazai...

NAFDAC ta ce kar ƴan Najeriya su riƙa cin abincin da ya wuce kwana 3 a firij

Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ta bukaci ‘yan Najeriya da su guji ajiye dafaffen abinci a cikin firiji sama da kwanaki...

Ƴanbindiga sun kashe mutane a Jihar Kaduna

An tabbatar da mutuwar mutane shida yayin da wasu da dama tare da yin garkuwa da su a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka...

Obasanjo ya kai wa Remi Tinubu ziyara

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara ga, Oluremi Tinubu mai ɗakin shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu . Obasanjo ya ziyarci matar shugaban ƙasar a...