Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar komawa makaranta domin karatun dokar shari’a.
Sarkin ya yi wannan bayani ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, bayan kammala karatunsa a aji.
A cewarsa, doka fanni ne da mutane da dama ke shiga bayan sun kai matakin ritaya, domin tana shafar kusan dukkan bangarorin rayuwa.
Ya ce, “Babu abin da za ka yi ba tare da doka ba. Doka ce ke nuna yadda ake tukin mota a hanya. Doka ce ke tsara yadda ake tafiyar da iyali da aure. Doka na kula da kwangila, filaye, kadarori da gado.”
Sarkin ya kara da cewa, “Doka muhimmin fanni ne da ya kamata kowa ya san shi gwargwadon iko. Ranar da babu doka da oda, masu karfi sukan yi abin da suka ga dama, marasa karfi kuma su sha wahala. Doka ita ce kariya da ginshikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a al’umma.”
Sanusi II ya kuma bayyana cewa karatu ya kasance wani bangare na rayuwarsa tun da dadewa.
Rahoton ya nuna cewa Sarkin Kano na ci gaba da halartar karatun dokar shari’a, lamarin da ya jawo martani daga jama’a da dama.
Dalilin Da Ya Sa Na Koma Karatu a Jami’a—Sarkin Kano Sanusi II

