Dalibin Jami’a Ya Rasu Bayan Dukan Da Aka Yi Masa Saboda Zargin Satar Waya

Wani dalibi na Jami’ar Najeriya Nsukka (UNN) ya rasa ransa bayan dukan da ake zargin ‘yan uwansa dalibai suka yi masa a ɗakin kwanan maza na Eni Njoku, sakamakon zargin satar waya.

Har yanzu ba a bayyana sunan mamacin ba, amma rahoton da fitaccen mai yada labarai a Facebook, Sen Chijinkem Ugwuanyi, ya wallafa a ranar Alhamis ya nuna cewa dalibin an jawo shi daga dakin kwana sannan aka yi masa duka sosai, wanda ya jefa shi cikin mummunan yanayi.

A cikin rubutunsa ya ce: “UNN Student Dies After Beating at Eni Njoku Hostel.

“A sad incident was reported at Eni Njoku male hostel in UNN, where a student allegedly died after being beaten by other hostel residents over a suspected phone theft.

“The student was dragged out and beaten, which left him with serious injuries. Efforts to save his life did not succeed.

“Authorities of @University of Nigeria Nsukka will now do like nothing happened inside #UNN.”

A lokacin da aka wallafa labarin, hukumar jami’ar ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba. Mai rikon mukamin Jami’in Hulɗa da Jama’a na UNN, Inya Agha Egwu, ya shaida cewa yana Lagos, don haka bai iya bayar da bayanai tukuna ba.

Sai dai wani babban malami a jami’ar ya tabbatar da faruwar abin, inda ya bayyana mamakinsa. Ya ce: “Yes, the incident happened. It was a very big shock that such would happen in a university community. The individuals involved must be punished.”

Hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

More from this stream

Recomended