Dalibai 287 Aka Sace Tare Da Kashe Ɗan Bijilante 1 A Kuriga A Cewar Wani Malamin Makaranta

Sani Abdullahi malami a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kuriga dake ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna ya ce ɗalibai 287 ne ba a gansu ba bayan da ƴan bindiga suka kai farmaki garin ranar Alhamis da safe.

Abdullahi wanda ya yi magana lokacin da gwamnan jihar Kaduna,Mallam Uba Sani ya ziyarci garin bayan faruwar lamarin ya ce ƴan bindigar sun farma makarantun firamare da sakandaren da misalin ƙarfe 08:00 na safe.

Malamin ya ce an kashe wani mamba na ƙungiyar bijilante ta Kaduna State Vigilante Service (KADVS) a ƙoƙarin da yayi na tunkarar ƴan bindigar.

“A GSS Kuriga daliɓai 187 ne ba a gansu ba a yanzu haka. A makarantar firamare dalibai yara 125 ne suka ɓace da farko amma 25 daga ciki sun kubuta sun dawo gida” Abdullahi Ya faɗawa gwamnan.

Malamin ya ce ya isa makarantar da misalin ƙarfe 07:47 na safe inda ya shiga ofishin mai riƙon muƙamin shugaban makarantar domin ya saka hannu a rijista lokacin da ƴan fashin dajin suka yiwa makarantar ƙawanya.

Da yake magana kan harin gwamnan jihar Kaduna ya ce ” Tun lokacin da na samu baƙin labarin faruwar lamarin hankalina ya kasa kwanciya saboda duk wani ɗa da yake jihar Kaduna ɗana ne.Saboda haka bana son ku samu damuwa,”

“Sai muyi addu’ar Allah Ya kawo mana ɗauki. A namu ɓangaren a matsayin gwamnati baza mu gajiya ba har sai yaran nan sun dawo gida.”

Gwamnan ya yi alƙawarin gina ofishin ƴan sanda a garin da kuma samar da sansanin soja na dindin.

More from this stream

Recomended