
Dakataccen gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya dawo birnin Fatakwal a ranar Juma’a bayan hutun mako biyu da yayi a kasashen waje.
Fubara ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa dake Fatakwal da misalin karfe 07:00 na dare.
A lokacin da yake kasar waje rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya gana da shugaban masa, Bola Ahmad Tinubu a kasar Birtaniya.