Dakarun sojan MNJTF sun kashe ƴan ta’adda 4 a Borno

Dakarun sojan rundunar MNJTF ta dakarun haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa dake yaƙi da ƴan ta’adda a yankin tafkin Chadi sun samu nasarar kashe ƴan ta’adda huɗu a ƙauyen Yashinti dake ƙaramar hukumar Nganzi ta jihar Borno.

Dakarun sun farma ƴan ta’addan ne a ranar 18 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 06:12 na yamma biyo bayanan sirri da suka samu dake nuna cewa akwai ayyukan ƴan ta’adda a yankin.

Wasu majiyoyin bayanan sirri na sojoji sun bayyana cewa sojojin sun yi gaggawar zuwa yankin inda suka yi musayar wuta har ta kai ga kisan ƴan ta’addar huɗu.

Kayan da aka samu a wurin musayar wutar sun haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, gida zuba harsashin AK-47 guda 3.

More from this stream

Recomended