Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya ta 3 Division da ke aiki a karkashin rundunar hadin gwiwa ta Operation Enduring Peace sun kai samame wata maboyar masu garkuwa da mutane a Jihar Filato, inda suka cafke wasu mutane tare da kwato makamai.
An gudanar da samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan wata kungiyar masu garkuwa da mutane da ke aikata laifuka a yankin kauyen Lantom da ke Gundumar Kadarko a Karamar Hukumar Wase.
Masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Majiyoyin tsaro sun shaida masa cewa an kai samamen ne a ranar 6 ga watan Janairu, inda dakarun suka cafke mutum hudu da ake zargin mambobin kungiyar ne.
Makaman da aka samu sun hada da bindiga kirarriya da aka kera a gida, gatari da kuma adda.
Binciken farko-farko ya nuna cewa mutanen da aka kama na da hannu a wasu manyan laifukan garkuwa da mutane da fashi da makami da ake yi a Kadarko da wasu al’ummomin da ke makwabtaka da yankin.
Majiyoyin sun kara bayyana cewa wasu mambobi biyu na kungiyar sun tsere a yayin samamen, inda suka gudu da wata bindigar AK-47 da ake zargin mallakin kungiyar ce.
A yayin tambayoyi, wadanda aka kama sun bayyana wurin da ake boye wasu makamai da alburusai, tare da amincewa da kai dakarun wani wuri da ake zargin wata maboyar kungiyar ce a wajen garin Kadarko.
Sai dai a yayin da suke jagorantar dakarun zuwa wurin, an ce sun yi yunkurin kwace makami daga hannun wani jami’in tsaro domin tserewa.
Nan take dakarun suka dauki matakin gaggawa, inda suka hallaka su a wurin.
Rahotanni sun nuna cewa dukkan makaman da aka kwato na hannun dakarun sojin ke nan, yayin da ake ci gaba da gudanar da wasu samame domin cafke sauran ‘yan kungiyar da suka tsere tare da kwato makaman da suke dauke da su.
Dakarun Soja Sun Tarwatsa Maboyar Masu Garkuwa da Mutane a Filato, Sun Kwato Makamai

