
Dakarun rundunar jami’an tsaron haɗin gwiwa ta JTF a jihar Kebbi sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin ƴan ta’addan kungiyar Lakurawa ne a yankin Rubin Bisa da Fana dake ƙaramar hukumar Dandi ta jihar Kebbi.
A wata sanarwa da Abdulrahaman Zagga daraktan ayyukan tsaro na gwamnatin jihar, Kebbi ya fitar ya ce sauran mayaƙan kungiyar sun tsere da raunin harbin bindiga a yayin da aka gano tarin wasu makamai masu yawan gaske.
Ya ce an kai musu farmaki ne a ranar Laraba biyo bayan bayanan sirri da aka samu akan ayyukan ƴan ta’addan.
Ya ƙara da cewa shugaban ƙaramar hukumar, Dandi, Dr Mansur Kamba shi ne ya kai ƙorafi akan ayyukan ƴan ta’addan ƙauyukan Fana da Rubin Bisa.