Dakarun Najeriya sun kai farmaki wa ƴan’adda a Borno, wani kwamanda ya miƙa wuya

Rundunar sojin Najeriya ta sanar a ranar Lahadin cewa dakarunta sun yi nasarar kashe wani fitaccen kwamandan kungiyar Boko Haram, Abu Rijab da wasu mayakan ta’addanci a wani samame da suka kai ranar Asabar.

An bayyana hakan ne a wani sako da aka wallafa a kan shafin sojin Najeriya na X, inda ya ce an kai farmakin ne a Bula Daloye da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno.

Sojojin sun ce nasarar da aka samu ta zo ne baya ga mika wuya da ‘yan ta’adda da dama da iyalansu suka yi ga sojojin sakamakon ci gaba da matsin lamba da suke sha a yankunansu. 

Rundunar ta ce sojojin sun kuma kama wasu da ake zargi da aikata laifuka tare da kwato makamai da alburusai.

“Bayan wani kazamin musayar wuta da aka yi, sojojin sun yi galaba a kan ‘yan ta’addan, inda suka kashe uku, ciki har da wani kwamandan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, Abu Rijab. 

“Ofireshan din ya kai ga kwato bindigogin AK-47 guda biyu da wayoyin hannu.

“Bugu da kari, ‘yan ta’adda takwas da iyalansu sun mika wuya ga sojoji a karamar hukumar Gwoza.

More from this stream

Recomended