Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala ‘yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar, Guruf Kaftin Kabiru Ali, ya fitar ranar Alhamis ta ce an kashe ‘yanbindigar ne a wani hari ta sama da jami’an rundunar suka kai musu ranar Laraba 11 ga watan Satumba, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.
Kafofin yada labaru sun ambato sanarwar na cewa, “An kai harin ne kan ‘yanbindigar a yankin Bassa, bayan da jami’anmu suka samu kiran gaggawa daga sauran jami’an tsaro a yankin.
“A lokacin da sojojin saman suka isa yankin, jirginsu ya hangi ‘yan bindigar su fiye da 100 suna musayar wuta da jami’an tsaron da ke ƙasa, bayan jami’anmu sun fahimci inda sojoji suka tsaya, sai jirginmu ya buɗe wa ‘yanbindigar wuta bayan ya gono inda su ma suka tsaya.
“Harin jirgin ya yi nasara, inda ya kashe gomman ‘yanbindigar, kuma kawo yanzu mun gano gawarwaki 28 a yankin, inda kuma wasu da dama suka ƙone tare da babura da makamansu.”