Da ɗumi-ɗumi: Ododo na APC ya lashe zaɓen gwamna a Kogi

An bayyana dan takarar gwamnan jam’iyyar All Progressives Congress, Usman Ododo, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi da aka kammala ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ododo ya samu kuri’u 446,237, inda ya doke abokin hamayyarsa Murtala Ajaka na jam’iyyar Social Democratic Party, wanda ya samu kuri’u 259,052, yayin da Dino Melaye na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 46,362.

Hakan dai na zuwa ne duk da cewa INEC ta sanar da cewa za a sake gudanar da sabon zabe a wasu rumfunan zabe a karamar hukumar Ogori/Magongo da ke jihar a ranar 18 ga Nuwamba, 2023.

More from this stream

Recomended