DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta tabbatar da Bala Mohammed da kujerarsa ta gwamnan Bauchi

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben amma Sadique Abubakar, takwaransa na jam’iyyar APC ya ki amincewa da sakamakon ya garzaya kotu.

Kotu sauraron ƙararrakin zabe da kotun daukaka kara sun tabbatar da nasarar gwamnan, amma Abubakar ya garzaya zuwa kotun koli.

More from this stream

Recomended