
Hukumar NCDC dake yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce mutane 138 ne suka mutu sanadiyar kamuwa da cutar zazzabin Lassa a shekarar 2025.
A rahotonta na baya-bayannan kan halin da ake ciki NCDC ta ce mutane 717 ne aka tabbatar sun kamu da cutar daga farkon shekara ya zuwa ranar 04 ga watan Mayu inda Ondo, Edo, Bauchi, da Benue suka samu wadanda suka kamu da cutar a wannan makon.
Hukumar ta ce duk da cewa adadin sababbin masu kamuwa da cutar ya ragu kadan daga 11 zuwa 10 a cikin makon da ya wuce jumullar yawan wadanda suka mutu abun damuwa ne.
Rahoton ya ce kaso 71 na dukkanin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar sun fito ne daga jihohin Ondo, Bauchi da kuma Taraba.
Rahoton ya kara da cewa yan shekarun 21 zuwa 30 su ne rukunin mutanen da cutar tafi kamawa.