Cutar zazzaɓin Lassa ya kashe mutane 12 a Ondo

Barkewar annobar cutar zazzaɓin Lassa ta halaka mutane 12 a yayin da aka tabbatar da cewa mutane 112 suka kamu da cutar..

Mai riƙon muƙamin babban mai ƙididdiga na jihar,Olusola Ajayi shi ne ya bayyana haka lokacin da yake wa ƴan jaridu jawabi.

Inda ya ce jumillar mumutane 353 aka bada rahoton cewa ana zargin suna da ɗauke da cutar.

Da yake bayyana halin da ake ciki a matsayin abun damuwa ya shawarci ma’aikatan hukumar kwashe shara ta jihar da su ruɓanya ƙoƙarin da suke kana su haɗa kai da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya domin samar da muhalli zaɓtatacce.

Ya jadda muhimmanci ɗaukar matakai domin hana cutar yaɗuwa da kuma kare lafiyar al’umma.

More from this stream

Recomended