Cutar sanƙarau ta kashe mutane 26 a Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 26 biyo bayan zargin barkewar cutar sanƙarau a kananan hukumomin Aleiro, Gwandu da kuma Jega.

Cutar sanƙarau cuta dake shafar ƙwaƙwalwa da kuma laka tana kuma yaɗuwa ta hanyar kusantar wanda ke ɗauke da cutar.

A cewar jami’an kiwon lafiya alamomin cutar sun haɗa da zazzaɓi, ciwon kai mai tsanani, ƙwannafi, amai da kuma ƙagewar wuya matuƙar ba ayi maganinta da wuri ba ta kan kaiwa ga mutuwa.

Gwamnatin jihar ta bawa al’ummar jihar tabbacin cewa an ɗauki matakan daƙile yaɗuwar cutar ta hanyar ƙara sanya idanu da kuma wayar da kan al’umma.

Har ila yau hukumomi sun shawarci mazauna jihar da su gaggauta neman kulawar jami’an kiwon lafiya matukar sun ji wasu daga cikin alamomin cutar.

More from this stream

Recomended