Cutar Kwalara na kara kamari a Najeriya

[ad_1]

Kano

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dubban mutane ne suka kamu da cutar a Kano

Mahukunta a Najeriya sun bayyana cewa akalla mutum dari uku ne suka harbu da cutar kwalara a kasar, kuma hamsin daga ciki sun fito ne daga jihar Kano.

Tun a farkon wannan shekarar ne cutar ta fara bulla, wadda da sannu ta shafi jihohi goma sha bakwai, ciki har da Abuja, babban birnin kasar.

Masana sun ce rashin tsabtar abinci da ruwan sha ne ke haddasa cutar ta kwalara.

A jihar Kano dubban mutane ne suka kamu da cuta mai alaka da amai da gudawa, amma kadan daga ciki ne aka tabbatar da cewa sun harbu da cutar kwalara, daga watan Janairun wannan shekarar zuwa watan Yulin da ya wuce.

Kwamishinan lafiyar jihar Kano, Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana haka, a wata ganawar da ya yi da manema labarai, inda wakilan kungiyoyin gaji na kasa da kasa ciki har da wakilin Hukumar Lafiya ta duniya suka halarta.

A Najeriyar dai kusan kowace shekara sai an samu bullar cutar kwalara, musamman ma a wannan lokaci na Damina.

Jihohin da cutar ta shafa a wannan shekarar sun hada da Adamawa da Anambara da Bauchi da Borno da Ebonyi da Gombe da Jigawa da Kaduna da Kano da Katsina da Kogi da Nasarawa da Neja da Filato da Yobe da Zamfara da kuma Abuja, babban birnin kasar.

Bullar cutar kwalarar dai na kara fito da kalubalen da gwamnatoci ke fuskanta na samar da ingantaccen ruwan sha ga al`umma, da kuma bukatar ci gaba da wayar da kan jama`a a kan hanyoyin tsabtace kayan abinci.

Kodayake, jihar Kano a nata bangaren, tun bullar cutar, a farkon wannan shekarar ta fara gudanar da tarukan wayar da kan jama`a a kan cutar, da wasu sakonni ta kafafen yada labarai.

Sai dai alamu na nuna cewa akwai bukatar a matsa-kaimi, kasancewar a makon da ya wuce ma an samu mutum biyu da aka tabbatar da cewa sun harbu da cutar.

[ad_2]

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...