Cutar Korona : Mmutum miliyan biyu za su iya mutuwa saboda korona — WHO

Takunkumi

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce akwai yiwuwar cutar korona ta hallaka sama da mutane miliyan biyu, matsawar ba a samu hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya don dakile ta ba.

Dama tuni mutum miliyan daya sun mutu, a kasashen da cutar ta yadu a duniya.

Daraktan agajin gaggawa na hukumar Michael Ryan, ya ce a halin yanzu, akwai yiwuwar karin mutum miliyan daya su mutu, la’akari da matakin cutar da ake kai a yanzu haka.

Amurka ce kasar da tafi fama da korona, kuma kawo yanzu ta hallaka fiye da mutum dubu dari biyu a can.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina – sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi – za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. – akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

Alamomin cutar coronavirus

Da alama tana farawa ne daga zazzabi, sannan sai mutum ya soma tari.

Bayan mako guda, mutum zai rika fuskantar yankewar numfashi.

Don haka ya kamata mutum ya je asibiti idan ya fuskanci irin wadannan alamomi.

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...