Muhammad Ali Dastak sabon zaɓaɓɓen dan majalisar dokokin kasar Iran ya mutu sanadiyar cutar Corona.
Dastak wanda aka zaba kwanan nan a matsayin wakilin Astan Ashrafieh ya mutu ranar Asabar da safe. Yan kwanakin da suka wuce ne aka tabbatar yana dauke da cutar bayan da aka gwada shi.
Kianush Jahanpur, mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta kasar, ya ce cutar ta kashe a kalla mutane 43 cikin mutane 593 da aka samu suna dauke da ita.
“Abin takaici mutane 9 sun mutu sanadiyar cutar cikin sa’o’i 24 da suka wuce yawan mutanen da suka mutu yanzu ya kai 43,” ya ce.
Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa mutane sama da 210 ne suka mutu cikin wadanda suka kamu da cutar.