
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Sufaniya na daya daga cikin kasashen da annobar cutar korona ta fi shafa kuma tana cikin wadanda ke tsananin bukatar kayan aikin asibiti, musamman a yankunanta da annobar ta daidaita.
Amma kokarin samun kayan aiki ya fuskanci koma baya dalilin takun saka tsakaninta da gwamnatin Turkiyya, inda ta kwace daruruwan na’urorin taimakawa marasa lafiya yin numfashi da wasu kungiyoyi suka yi daga yankuna uku a Sufaniya.
Kafofin yada labaran Sufaniya sun ce wannan “sata” ce.
Bayan kusan mako guda ana ce-ce-ku-ce, ma’aikatar harkokin wajen Sufaniya ta karbo kayan. Amma wannan wani misali ne kawai na yadda cutar korona ke rura wutar rikicin diflomasiyya a fadin duniya.
A ina rikice-rikicen ke faruwa?
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Babu shakka cacar bakin da aka dade ana yi tsakanin Amurka da China ta dauki hankali, musamman idan aka duba lokutan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar dakatar da tallafin kudi ga Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO bisa dalilin da ya ce hukumar ta ta’allaka kan China.
Amma an kai gabar tashin hankali a wani wurin. Kuma wannan karon bai shafi China ba, wacce ke fuskantar zarge-zargen rage alkaluman yawan mutanen kasarta da cutar ta kama.
“A iya cewa kamata ya yi a yanzu mu ga kasashe suna hada karfi da karfe a wannan lokaci da muke yakar annobar,” in ji Sophia gaston, wata mai bincike a fannin zamantakewa da siyasa a jami’ar London.
“A zahiri, wannan annobar ta tirsasa wa kasashe janye jikinsu kuma haifar da gasa maimakon hadin kai.”
Misali daya shi ne rikicin da ke gudana tsakanin kasashen Taryyar Turai.
Lokacin da yawan mutane masu dauke da cutar korona a Italiya ya karu sosai, kasar ta nemi agajin kayan aikin asibiti daga makwabtanta. Daga Jamus har Faransa sun yi kunnen uwar shegu, suka haramta fitar da kayan da Italiyar ke bukata.
“Lallai ne wannan ma alama ce mai kyau ta hadin kan Turai,” in ji jakadan Italiya a Brussels Maurizio Massari.
‘Yan Italiya ba su ji dadin sa-toka sa-katsin da annobar ta haifar a tsakaninsu da Jamus ba saboda tana daga bangaren da ke sukar kudirin samar da agaji ga kasashen Tarayyar Turai da annobar ta fi shafa.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
“Diflomasiyyar China ta takunkumin fuska
Kasashen Netherlands da Austria da Finland sun fito fili sun soki shirin, yayin da Sufaniya da Faransa da Belgium da Girka da Ireland da Portugal da Slovenia da Luxembourg duk sun goyi bayan shirin. Wannan ya nuna matukar rarrabuwar kai a tsaknain kasashen EU.
Italiya babbar misali ce kan abin da kwararru suka bayyana a matsayin “diflomasiyyar takunkumin rufe fuska ta China”: bayan shawo kan cutar korona a cikin kasarta, gwamnatin China ta yi wa kasashe da dama yayyafin kayan agaji salo-salo don shawo kan cutar – cikin wadannan kasashen kuwa har da Rasha.
Italiya ta samu agajin kayan aikin asibiti da kayan gwaji; kai har ma da tawagar likitoci ‘yan China da ake wa kirarin cewa jarumai ne. Wato har sai da aka rika yayata wani maudu’I a shafukan sada zumunta na Italia mai taken #garzieCina wato ‘Mun gode China’ kenan da yaran Italiya.
Gesu Antonio Baez, shugaban kamfanin Pax Tecum da ke birnin Landan wanda ya kware wajen ci gaban batutuwan diflomasiyya, ya ce China na kokarin maye gurbin da Amurka ta bari ne a fagen shugabancin duniya – wanda taken Donald Trump na “America First” (wanda ke nufin tsananin kishin kai da dogaro da kai) ya kara lalatawa tun hawansa mulki a 2016.
Matsayar Amurka kwata-kwata ba ta nuna son a zauna lafiya ba: baya ga takun saka tsakaninta da China, Trump ya kai wa hukumomin Jamus har wuya lokacin da ya yi kokarin samun karfin iko shi kadai kan wani rigakafin cutar korona da wani kamfanin sarrafa magungunan Jamus din ya samar.
A baya-bayan nan, shugaban ya aike wa Indiya gargadi bisa matakinta na hana fitar da magungunan zazzabin maleriya na hydroxychloroquine, wanda ake gwadawa a matsayin maganin Covid-19.
“Amurka ba ta taka wata rawar gani ba (a matsayinta na mai karfin fada a ji) yayin wannan annoba kuma a yanzu China na da damar maye wannan gurbin,” a cewar Baez.
“Diflomasiyyar takunkumin rufe fuskar” ba ta kai tsaye ba ce, kamar yadda Brazil ta nuna. Yadda ake ganin China ta gaza shawo kan annobar Covid-19 da farko cikin gaggawa ya janyo mata zunde a tsakanin kasashen duniya, in ji Sophia Gaston.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Rikicin China da Brazil a shafukan sada zumunta
Ta ambaci wani rahoton leken asirin Amurka da ya zargi China da yin kumbiya-kumbiya kan yawan mutanen da suka kamu da wadanda suka mutu sakamakon korona – hukumomin Birtaniya ma sun nuna tantama kan alkaluman China.
“An dade da sa wa China ido a lokacin da ta fara wadannan ayyukan nata na ‘ganin ido’. Za ta fuskanci suka sosai idan asalin alkalumanta suka bayyana,” in ji Gatson.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Brazil ma wata kasa ce da ke tantama kan matsayin China: Da Chinar da Brazil din duk sun sha yin rikici tun barkewar annobar.
Har ta kai jami’an diflomasiyyar China da mutanen Shugaba Jair Bolsanaro na kut da kut suna sa-in-sa a shafukan sada zumunta.
A wani rikici na baya-bayan nan, ministan ilimi Abraham Weintraub ya takalo jami’an China da wani sako da ya wallafa a Twitter inda takwarorinsa na Asiya suka ce ya nuna wariyar launin fata.
“Irin wadannan kalaman ba su dace ba kuma suna matukar nuna wariyar launin fata,” in ji Ofishin Jakadancin China da ke Brasilia.
China ce babbar abokiyar kasuwancin Brazil – tana sayen kashe 80 cikin dari na waken suyar kasar, misali – kuma hukumomin lafiyar Brazil kawo yanzu na ta kokarin samun na’urorin numfashi na ventilator da sauran kayan aikin lafiya daga China kafin Weinstraub ya shiga tsakani.
Rura wutar dadaddiyar rikici
Gesu ya ce “Wannan ya nuna abin da ya sa ake bukatar diflomasiyya fiye da komai,”
“Kasashe na bukatar su duba yadda lamura ke tafiya sannan su kwantar da hankali ta hanyoyin da suka dace.”
Amma cutar ita kanta, tana kara iza wutar dadaddun rikice-rikice. Misali rikicin Colombia da Venezuela.
Hukumomin Colombia ba sa ganin gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela a matsayin sahihiyar gwamnati kuma kasashen biyu masu makwabtaka na karawa da juna bayan da ‘yan ciranin Venezuela da yawa suka tsallaka iyaka.
Mataki na baya-bayan nan ya zo ne ranar 1 ga watan Afrilu kuma tayin na’urorin gwajin Covid-19 guda biyu da Maduro ya yi wa takwaransa na Colombia, Ivan Duque ne ya tunzura hakan.
A kwanakin baya rahotanni sun ce na’urar gwaji daya tilo da Colombia ke da ita ta lalace.
Duque ya yi gum da bakinsa bayan da aka yi masa tayin, kuma wannan ya yi matukar bata wa jami’an Venezuela rai musamman ma mataimakiyar shugaba Delcy Rodriguez.
“Gwamnatin Ivan Duque ta ki karbar na’urori biyu daga hannun shugaba Maduro… wannan ya sake nuna rashin imanin Mista Duque da rashin damuwarsa kan al’ummar Colombia,” kamar yadda ta wallafa a Twitter.
A wata hira a rediyo da aka watsa ranar 7 ga watan Afrilu, Duque ya ce na’urorin “ba su dace da irin gwaje-gwaje da kayan aikin da ake amfani da su ba a Colombia”.
A Gabas ta Tsakiya, Qatar da Masar na rikici kan makomar ‘yan asalin Masar da suka makale a Qatar.
Hukumomin Qatar, wadanda ke fama da yawan mutane masu dauke da Covid-19 a kasashen yankin Gulf, sun shaida wa kafar watsa labarai ta Al Jazeera cewa hukumomin Masar sun ki amincewa da jirgin da aka yi wa ‘yan cirani shata.
Masar na cikin kungiyar kasashen Larabawa da tun 2017 suka yanke alakar diflomasiyya da Qatar bisa zargin cewa gwamnatinta na goyon bayan kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi.
Hakkin mallakar hoto
Handout
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Damarmakin yin rikici
Sai dai abubuwan da ke janyo rikice-rikice sun fi karfin takunkuman rufe fuska da hana zirga-zirga.
Ranar 18 ga watan Maris , wani rahoton Tarayyar Turai da aka aike wa manema labarai a asirce ya zargi kafofin yada labarai da Rasha ke ‘janye wa ra’ayi’, da ‘yada labaran karya’ kan cutar korona a yankin Yamma.
Wani mai magana da yawun gwamnatin rasha ya ce zargin “ba shi da tushe”.
Idan rarrabuwar kai na karuwa, wasu kwararru na ganin za a samu abubuwa masu kyau da za su fito daga annobar.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Annalisa Prizzon, wata mai bincike a wata cibiyar bincike ta ce annobar ta bayar da damar hadin kai mai amfani.
Ta ce “Rikicin na nuna cewa ba ko yaushe ne kasashen da suka ci gaba suke ‘kwararru’,” ba.
“Yadda China ta agaza wa Italiya da hanyoyin da ta bi wajen rage radadin annobar, ya kasance babban misali mai amfani.”
Amma Sophia Gaston na ganin akwai bukatar sake hada kai.
“Damar ta wuce, musamman ga kasashen Yamma a lokacin da ake nuna kishin talaka da kishin kasa,” a cewarta.
“Wannan lokaci ne na nuna karfin hadin gwiwa.”
Daga karshe ta ce “Maimakon haka, tsare-tsare da dama na kara lalata dangantaka tsakanin kasashe.”