HomeHausaCoronavirus ta bulla a Lagos: Hanyoyin 4 na kare kai daga cutar

Coronavirus ta bulla a Lagos: Hanyoyin 4 na kare kai daga cutar

Published on

spot_img
@

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.

Yaya zan kare kaina daga cutar?
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:
■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta
■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina – sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atisjawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.
■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.
■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi – za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. – akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakaniku za ta kai kafa uku.
Alamomin cutar coronavirus
Wadanne ne alamomin cutar?

  • Najeriya ta tabbatar da bullar Coronavirus a Lagos

Da alama tana farawa ne daga zazabi, sannan sai mutum ya soma tari.
Bayan mako guda, mutum zai rika fuskantar yankewar numfashi.
Don haka ya kamata mutum ya je asibiti idan ya fuskanci irin wadannan alamomi.

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this