Majalisar Wakilan Najeriya ta kaddamar da bincike game da wasu ‘yan kasar China da gwamnati ta kai kasar a watan jiya da sunan taimaka wa bangaren kiwon lafiya wajen yaki da annobar korona.
A baya-bayan nan dai ana ta ce-ce-ku-ce a kasar kan ‘yan kasar ta China musamman bayan da aka daina jin duriyarsu da kuma sanin aikin da suke yi a cikin Najeriya.
Wasu rahotanni a kasar ma na cewa wasu daga cikin ‘yan Chinar, ma’aikatan gine-gine ne ba likitoci ba, kuma hatta jami’an da ke yaki da cutar ta korona ba su da cikakkiyar masaniyar inda suke.
A cewar Honourable Abdulrazak Namdas, irin wadannan ce-ce-ku-cen da ake yi na daya daga cikin wannan na cikin dalilan da yasa majalisar wakilan kasar ta kaddamar da bincike domin gano gaskiyar al’amarin.
Namdas ya bayyana cewa tun bayan shigar ‘yan Chinar Najeriya, ba su sake jin labarinsu ba kuma ga shi cuta na ƙara yaɗuwa.
Ya bayyana cewa a wannan dalili ne ya sa majalisa ta ce da farko yakamata a gano a ina ‘yan Chinar suke? Da kuma ainahin me ya kawo su?
Ya bayyana cewa “‘yan Najeriya na da ‘yancin su san a ina mutanen nan suke don mu san sun zo da cuta ne ko ba su da shi.”