Gwamnatin Neja da ke tsakiyar Najeriya ta sanar da matakin sassauta umarnin hana fita da ta sanya tun bayan bullar annobar coronavirus a kasar.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Alhaji Sani Idris ya shaida wa BBC cewa tun da farko dai gwamnatin ta ba da umarnin hana tafiye-tafiye daga karfe takwas na safe zuwa takwas na yamma domin kare yada cutar.
A cewar kwamishinan, sauran dokokin da aka sa kamar na hana taruwa a makaranta da wuraren ibada suna nan daram.
Har yanzu dai ba a samu rahoton bullar cutar coronavirus ba a jihar duk da cewa jihar na makwabtaka da Abuja babban birnin kasar.
Ya ce gwamnati ta sha sassauta dokar hana fitar a lokuta daban-daban sakamakon bibiyar al’amuran da ke wakana a Abuja.
“Daga baya mun yi sassauci aka mayar da dokar daga karfe goma na safe zuwa takwas na dare sannan da muka ga iyakoki a bude ana shige da fice, sai muka sake mayar da dokar daga karfe goma na safe zuwa 12 na dare,”.
A cewarsa, tun daga lokacin gwamnatin jihar ta bijiro da tsare-tsare daban-daban da suka hadar da gudanar da bincike kan baki da suka shiga jihar.
“La’akari da yadda al’umma suka ba da goyon baya muka ga ya kamata a kara sassauta dokar,”. Kwamishinan ya ce matakin zai bai wa gwamnati damar fito da tsare-tsare masu muhimmanci.
“Akwai umarni da aka ba shugabannin ma’aikatun da za a bude, kowace ma’aikata za a tanadi abubuwa da ma’ikatan lafiya suka ba da shawara yadda za a wanke hannu da kiyaye cunkoso.”
“Matakin dakatar da tafiye-tafiye tsakanin makwabtan jihohi zuwa Neja har yanzu yana nan.”