Coronavirus: An killace wasu ‘yan China uku a Filato | BBC Hausa

.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ma’aikatar lafiya a jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya ta tabbatar da killace wasu ‘yan kasar China uku saboda fargabar coronavirus.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Nimkong Ndam ya tabbatar wa BBC da cewa lamarin ya faru ne bayan wasu ‘yan kasar Chinar uku da ke aiki a wani wurin hakar ma’adanai a garin Wase sun dawo daga tafiya.

Ya ce da isarsu kamfanin sai ‘yan uwansu ‘yan China wadanda ba su yi tafiya ba suka hana su shiga kamfanin sakamakon tsoron da suke yi ko kuma fargabar kada a ce sun dauko musu cutar coronavirus sun kawo musu.

Mista Ndam ya shaida cewa wannan dalilin ne ya sa ma’aikatar lafiya tare da hadin gwiwar hukumar da ke kula da shige da fice da kuma ‘yan sanda suka tura tawaga zuwa garin Wase domin likitoci su yi musu gwajin cutar ta coronavirus.

Kwamishinan ya bayyana cewa idan sakamakon gwajin ya fito, zai yi bayani dangane da ko suna da cutar ko babu.

Kwamishinan ya ce tun asali ma’aikatan hakar ma’adinai ‘yan China su ne suka tsare ‘yan uwansu kuma su ma za su kara karfafa hakan domin kada su fita su gauraya da sauran jama’ar gari.

Sai dai ya yi korafi dangane da ‘yan jaridu kan yadda suke zuzuta batun labarin ‘yan Chinan uku na jihar ta Filato inda ya ce a yi hakuri domin har yanzu ana bincike.

Tuni dama hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce cutar coronavirus ta kai wani matsayi na zama annoba a duniya saboda yadda take yaduwa.

An samu bullar cutar a Najeriya a ranar Juma’a, lamarin da ya jawo rudani a fadin kasar.

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar

Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

â–  Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina – sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

â–  Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

â–  Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi – za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. – akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

More News

DA ÆŠUMI-ÆŠUMI: DSS sun cafke Sowore a filin jirgin na Legas

Jami'an Hukumar Ƴansandan Farin-kaya ta DSS sun kama Omoyele Sowore, jagoran kungiyar  #RevolutionNow Movement da ke adawa da gwamnati a filin jirgin sama na...

Ƴan bindiga sun Æ™one ginin hedkwatar Æ™aramar hukuma tare da kashe jami’an tsaro

Ƴan bindiga sun kai farmaki hedkwatar ƙaramar hukumar, Isiala Mbano dake jihar Imo da tsakar daren ranar 3 ga watan Satumba inda suka ƙone...

An kama wasu Æ´anta’adda da ke da alaÆ™a da Turji

Akalla mayaka 18 da ke da alaka da fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji aka kama a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin...

Dakarun Najeriya sun kai farmaki wa Æ´an’adda a Borno, wani kwamanda ya miÆ™a wuya

Rundunar sojin Najeriya ta sanar a ranar Lahadin cewa dakarunta sun yi nasarar kashe wani fitaccen kwamandan kungiyar Boko Haram, Abu Rijab da wasu...