
Ofishin shiyar Kaduna na hukumar EFCC dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati sun kama, Mohammed Kabir Saad wani mai yin bidiyo a kafafen soshiyal midiya inda ake zarginsa da cin zarafin takardar kudin naira.
Saad ya dauki wani fefan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram da TikTok inda aka nuna shi yana watsi da takardar kudin naira a kasa yana kuma takasu da gangan tare da tsokanar jami’an hukumar EFCC kan su kama shi idan za su iya.
A karshe bayan gudanar da bincike tare da bin diddiginsa jami’an EFCC sun yi ram da shi a unguwar Tudun Wada dake Kaduna.
Hukumar ta EFCC ta bayyana cewa nan gaba kadan za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan an kammala bincike.