Cikom shekara 2, an hallaka mutum 387 a ƙananan hukumomin Kauru da Zango, in ji El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya faɗa a yau Laraba cewa a cikin shekaru biyu da suka wuce, an kashe mutane 387 a rikice-rikicen da aka yi a ƙananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da kwamishinan tsaro na cikin gida, Samuel Aruwan, ya wakilce shi a fadar Agwatyap da ke Zangon Kataf.

Jihar Kaduna dai na cikin jerin jihohin da tashe-tashen hankula suka addaba a yankin Arewa.

More from this stream

Recomended