Christian Eriksen: Inter Milan na daf da soke yarjejeniya da dan wasan

Christian Eriksen
Christian Eriksen ya yanke jiki ya fadi a fili ana tsaka da wasa a gasar Euro 2020

Inter Milan na shirin kawo karshen yarjejeniyar da ke tsakaninta da Christian Eriksen.

Dan kwallon tawagar Denmark bai sake buga tamaula ba, tun bayan da ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da wasa a Euro 2020 a karawa da Finland a cikin watan Yuni.

A baya an sanar cewar yana atisaye shi kadai a wani wuri da aka tanada a Denmark.

Babu inda aka tabbar kan ko yaushe ne Eriksen zai koma taka leda a matakinsa na kwararren dan wasa.

Kuma koda dan wasan mai shekara 29 zai so ya ci gaba da taka leda, hakan ba zai yi wu ba a gasar Serie A, har sai an cire masa abinda aka saka masa don taimaka wa zuciyarsa bugawa kamar yadda ya kamata.

Inter Milan na tausayawa dan kwallon kan halin da ya shiga, tana kuma bin hanyoyin da suka da ce don kawo karshen kwantiragin da ke tsakaninta da dan wasan

Eriksen ya koma Inter Milan daga Tottenham a Janairun 2020 kan yarjejeniyar shekara hudu.

More from this stream

Recomended