China ta yi ramuwa kan rufe mata ofishin jakadanci a Amurka

The US Consulate-General in Chengdu is pictured on July 23, 2020 in Chengdu, Sichuan Province of China.

Bayanan hoto,
Ofishin jakadancin Amurka na Chengdu

China ta mayar da martani kan rikicin diflomasiyyarta da Amurka wanda ke Æ™ara ta’azzara.

Mahukuntan Beijing dai sun buƙaci Amurka ta rufe ofishin jakadancinta da ke Chengdu, a kudancin ƙasar.

China dai ta bayyana al’amarin a matsayin halartaccen mataki da ya zama dole.

A wani abu mai kama da idan ka ce kule zan ce ma cas, yanzu dai China ta mayar da martani kan rufe ofishin jakadancinta da Amurka ta ba da umarni a Houston.

China dai ta buƙaci ita ma Amurka ta rufe nata ƙaramin ofishin jakadancin da ke tsakiyar lardin Sichuan na kudancin ƙasar.

Tun a tsakiyar 1980 ne, Amurka ta buÉ—e ofishin jakadancin na Chengdu.

Daga cikin ayyukansa akwai lura da ayyukan sa-idon gwamnatin Amurka da kuma dangantakarta da yankin Tibet, wanda tsawon lokaci ke fafutuka don ganin hukumomin China sun ba shi Æ™arin ‘yanci.

Matakin na zuwa ne bayan Amurka ta umarci China ta rufe ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Houston, inda ta yi iƙirarin cewa matakin yunƙuri ne na kare sirrin Amurkawa da haƙƙin mallakar ƙirƙire-ƙirƙirensu.

China dai ta bayyana matakin a matsayin wani gagarumin keta dokar ƙasashen duniya.

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...